in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru: Zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka zai biya bukatun jama'a
2018-05-21 11:26:22 cri

A ranar Asabar da ta gabata, bangarorin Sin da Amurka sun kammala shawarwari kan harkokin tattalin arziki da cinikayya, inda suka cimma matsaya, tare da gabatar da wata hadaddiyar sanarwa a birnin Washington na kasar Amurka. Daga bisani, a jiya Lahadi, wasu kwararru a fannin tattalin arziki da suke halartar wani taron dandalin kasa da kasa a birnin Beijing na kasar Sin, sun nuna farin cikinsu dangane da ra'ayi daya da Sin da Amurka suka cimma. A jiya Lahadi, an kaddamar da taron dandali na Sin da dunkulewar duniya karo na 4, mai taken "daidaita tsari da ciyar da harkoki gaba: makomar manufar gyare-gyare da bude kofa gami da dunkulewar kasashen duniya waje guda", a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kwararru masu halartar taron sun bayyana farin cikinsu game da ra'ayi daya da Sin da Amurka suka cimma, game da magance ta da wani yakin ciniki. A ganin Scott Kennedy, mataimakin darektan sashin "Freeman Chair in China Studies" karkashin cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta CSIS ta kasar Amurka, yadda aka cimma matsaya a wannan karo wani sakamako ne mai kyau. A cewarsa, "Bisa wannan sakamako na farko da aka samu, dukkan bangarorin Sin da Amurka, sun yi alkawarin cewa ba za a shiga yakin ciniki, ko kuma daukar wani mataki na radin kai ba.

A ganina wannan wani sakamako ne mai faranta rai." Bisa hadaddiyar sanarwar da kasashen Sin da Amurka suka fitar, kasar Sin za ta kara sayen kayayyaki da hidimomin da kasar Amurka ke samarwa, don biyan bukatun al'ummar kasar Sin, da taimakawa samun ci gaban tattalin arzikin kasar mai inganci. Haka zalika, za a kara baiwa kasar Amurka karin damammakin fitar da amfanin gona da albarkatun makamashi.

Dangane da wannan yarjejeniya, Mista Fu Chengyu, tsohon shugaban kamfanin mai na SINOPEC na kasar Sin, ya bayyana cewa, "Fannoni 6 da aka tabo a cikin hadaddiyar sanarwa da kasashen Sin da Amurka suka gabatar, sun nuna wani sakamako mai kyau da aka samu, wanda ya shafi hadin gwiwa da cin moriya tare. Hakika huldar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, ba ta tsaya kan ciniki kawai ba, maimakon haka ta shafi sauyawar yanayin huldar kasa da kasa."

A nasa bangare, Long Yongtu, tsohon babban sakataren dandalin tattaunawar tattalin arzikin Asiya na Boao, ya ce yadda kasashen Sin da Amurka suka cimma ra'ayi daya a wannan karo zai amfani junansu. A cewar sa, "Dalilin da ya sa kasashen Sin da Amurka suka cimma matsaya a wannan karo, shi ne kasancewar shugabannin bangarorin 2 suna da cikakkiyar niyyar samun wannan sakamako, sa'an nan dukkan al'ummomin kasashen 2 suna bukatar cimma wannan daidaito. Tsarin da ake bi na samun dunkulewar kasa da kasa ya riga ya hada moriyar kasashen 2, da ta jama'arsu, waje guda. Domin wannan dalili ne, kasashen 2 suka zabi wata turbar da za ta kai su ga wata makoma mai kyau, inda za a tabbatar da moriyar dukkan bangarorin 2."

Ban da haka, mista Long ya kara da cewa, ta la'akari da yadda manufar gyare-gyare da bude kofa ta kasar Sin ta shiga wani sabon mataki, ya kamata a daidaita manufofinta na cinikayya da kasashen waje. A ganinsa, a lokacin baya, kasar Sin na bukatar fitar da kayayyaki don samun karin kudin musanya. Sai dai a yanzu kasar na son dora muhimmanci iri daya kan fannonin fitar da kaya da na shigo da kaya. Har ma za ta kara habaka harkar shigo da kaya, don biyan bukatun jama'ar kasar na samun kayayyaki da hidimomi masu inganci.

Sa'an nan a nashi bangare, mista Qian Jian'nong, shugaban kamfanin zuba jari na FOSUN, ya ce, duk da cewa a kan samu rikicin ciniki tsakanin kasashe daban daban, amma karkashin wannan alama, za a iya ganin yadda ake zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen. Saboda haka kamata ya yi, kamfanonin kasar Sin su kara inganta harkokinsu, da neman hadin gwiwa da karin abokai a nan gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China