in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Sin sun cimma matsaya game da takaddamar cinikayya
2018-05-21 09:52:04 cri
Sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin, ya ce kasar sa da Sin sun cimma muhimmiyar matsaya, game da takaddamar cinikayya da tattalin arziki.

Mr. Mnuchin ya bayyana hakan ne jiya Lahadi, yayin wata zantawa da kafar watsa labarai ta Fox News, yana mai cewa sassan biyu sun amince su dakatar da sanyawa juna takunkumin cinikayya.

Mnuchin ya ce Amurka da Sin sun cimma matsaya mai gamsarwa game da wannan batu. Kaza lika sassan biyu za su ci gaba da tuntubar juna game da batutuwa na raya cinikayya.

A ranar Asabar ne kasashen biyu suka fidda wata hadaddiyar sanarwa game da cudanyar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, suna masu tabbatar da kudurin su na dakatar da yakin cinikayya. Kasashen biyu sun kuma amince da daukar matakan rage gibin kasuwanci tsakaninsu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China