in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da samun sabon rahoton bullar cutar Ebola 4 a arewa maso yammacin DRC
2018-05-20 12:58:52 cri
Ministan lafiya na jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, Oly Ilunga, ya sanar da cewa an sake samun sabon rahoton bullar cutar Ebola 4 a lardin Equateur dake arewa maso yammacin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo.

Sanarwar ta ce an tabbatar da sabbin rahotannin bullar cutar 4 ne a cibiyar lafiya ta Iboko, daya daga cikin shiyyoyin kiwon lafiya da cutar ta fi shafa.

Kawo yanzu, adadin bullar cutar da aka samu ya karu daga 17 zuwa 21, tun bayan gwajin cutar na baya bayan nan da aka yi a lardin Equateur, bayan da aka sanar da bullar cutar a hukumance.

Wadannan sakamako suna daga cikin gwaje gwajen da ake gudanarwa a kullum a cibiyoyin gwaji na tafi da gidanka wanda tawagar jami'an ma'aikatar kiwon lafiyar kasar suke gudanarwa tare da hadin gwiwar tawagar jami'an hukumar lafiyar ta duniya (WHO), wadan da aka tura su yankunan tun bayan da aka ayyana bullar cutar a yankunan.

A cewar hukumar WHO, makasudun shirya gangamin rigakafin shi ne, domin yiwa al'ummar dake yankin da cutar ta bulla alluran rigakafi musamman mutanen da suka yi mu'amala tare da marasa lafiyan da suka kamu da cutar, ko kuma wadanda suka yi mu'amala da mutanen da suka yi mu'amala da marasa lafiyan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China