in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon alhini ga shugabannin Cuba da Mexico sakamakon hadarin jirgin sama da ya auku
2018-05-19 20:20:31 cri
Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon alhini ga babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba Raul Castrol, da shugaban kwamitin majalisar gudanarwar kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, da shugaban kasar Maxico Enrique Pena Nieto, dangane da hadarin jirgin sama na fasinjoji da ya auku a birnin Havana na kasar Cuba, wanda kamfanin jiragen saman kasar Cuba ya yi haya daga kasar Mexico.

A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kuma mika sakon alhini ga shugaban kwamitin majalisar gudanarwar kasar Cuba Miguel Diaz-Canel. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China