in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada aniyar yaki da hayaki mai gurbata yanayi don kyautata muhalli
2018-05-19 20:03:05 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da kokarinta na kawar da iska mai gurbata muhalli da kuma kyautata tsarin zamanantar da muhallin halittu zuwa sabon matsayi, shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin gudanar da wani taron tattaunawa na kasa game da batun kare muhalli wanda aka karkare a yau Asabar.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tafiyar da harkokin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma, da kuma zamanantar da tsarin muhallin halittu, shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, kana shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojojin kasar Sin, ya bayyana hakan ne a lokacin taron karawa juna sani na kasa na wuni biyu.

Xi ya ce, kasarsa za ta yi amfani da makamashi mai yawan gaske wajen zamanantar da tsarin muhallin halittu da kuma warware matsalolin da suka shafi muhalli, wanda ya yi daidai da tsarin shugabancin siyasa da manufofin jagorancin jam'iyyar CPC, da ma tsarin gurguzu baki daya, kana da irin nasarorin da aka cimma cikin shekaru 40 tun bayan aiwatar da sauye sauye a cikin gida da bude kofa ga waje.

Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gabatar da jawabi a yayin taron. Li, wanda mamba ne a zaunannen kwamitin gudanar da al'amurran siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta CPC. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China