Yau Asabar, kwamitin kula da harkokin zabe mai zaman kansa na kasar Iraki ya gabatar da sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar. Kawancen al-Sa'iroon dake karkashin shugabancin jagoran Shi'a Moqtada al-Sadr ta samu kujeru kimanin 54 daga cikin adadin kujeru 329 na majalisar dokokin kasar, wanda yake kan gaba a sauran kawancen da suka halarci zaben.
A bisa tsarin mulkin kasar Iraki, jam'iyyar da ta fi samun kujerun majalisar dokokin kasar tana da ikon nada firaministan kasar da kuma kafa gwamnati, kuma sabuwar kawancen da aka kafa bayan da aka gabatar da sakamakon zaben zai iya kasancewa a matsayin "babbar jam'iyya". (Maryam)