in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka kamu da cutar Ebola a DRC ya karu zuwa 14
2018-05-18 11:06:20 cri

A halin da ake ciki adadin mutanen da suka kamu da cutar Ebola a jamhuriyar demokaradiyar Kongo (DRC) ya karu zuwa 14 bayan da ma'aikatar lafiyar kasar ta tabbatar da sabbin rahotannin bullar cutar kimanin 11 da kuma rahoton hasarar rai guda a yankin arewa maso yammacin kasar.

Sanarwar da ma'aikatar lafiyar kasar ta bayar da yammacin ranar Alhamis ya nuna cewa, an samu sabbin rahotannin yaduwar cutar 11 da kuma mutuwar mutum guda a sanadiyyar cutar a garin Bikoro dake lardin Equateur, yankin da hukumomin kasar suka ayyana barkewar cutar a hukumance tun a ranar 8 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ce, adadin masu kamuwa da cutar Ebolan da ake zato a kasar ya tasamma 45, wanda ya hada 10 da ake zargin sun kamu da cutar, da kuma 21 da ba'a tabbatar da ko cutar ba ne, yayin da aka tabbatar da 14 sun kamu da cutar.

Ministan lafiyar kasar Oly Ilunga ya ce daga cikin mutane 25 da suka mutu a kasar, mutum guda ne aka tabbatar da mutuwarsa a sanadiyyar cutar ta Ebola, ya kara da cewa, kawo yanzu ba'a samu sabon rahoton wani jami'in lafiya da ya kamu da cutar ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China