Ministan harkokin waje, kuma Sakatare janar na fadar shugaban kasar, Kiridi Naby Youssouf Bangoura ne ya sanar da matakin cikin wata sanarwa da ya fitar a hukumance.
Bangoura, ya ce shugaban kasar Alpha Conde, ya umarci Firaministan da Gwamnatin mai barin gado, su kula da harkokin yau da kullum har zuwa lokacin da sabuwar Gwamnati za ta fara aiki.
A watan Junairun 2016 ne, dokar musammam ta shugaban Jamhuriyar Guinea, ta kafa Gwamnatin mai barin gado, da ta kunshi ministoci 33, ciki har da sakatare janar 2. (Fa'iza Mustapha)