in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Donald Trump ya gana da Liu He
2018-05-18 09:07:23 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya gana da Liu He, manzon musamman na shugaban kasar Sin, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin,kana mataimakin firaministan kasar Sin, mai jagorantar shawarwarin tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.

A ganawar tasu, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan dangantakar ciniki da tattalin arziki tsakaninsu. Mista Liu ya nuna cewa, ziyarar tasa a wannan karo, na da burin kara tuntubar juna ta fuskar tattalin arziki da cinikayya tare da Amurka, bisa matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a baya. Sin na fatan kara kokari da Amurka don daidaita wasu matsalolin tattalin arziki da cinikayya dake jan hankulan bangarorin biyu yadda ya kamata, bisa ka'idar adalci da moriyar juna, da kuma ba da tabbacin mai da hadin gwiwar cinikayya tsakaninsu, a matsayin wani muhimmin matakin ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba.

A nasa bangaren, Donald Trump ya ce, tabbatar da hadin gwiwa yadda ya kamata tsakanin kasashen biyu ta fuskar ciniki na da muhimmanci sosai, yana fatan kasahen biyu za su kara kokarin magance matsalolin dake tsakaninsu a fannin ciniki. Ya ce ya kamata, kasashen biyu su dora muhimmanci kan hadin gwiwar zuba jari ta fuskokin makamashi da sana'ar kere-kere, har ma da kara habaka cinikin amfanin gona, da kara ba da izni sayar da kayayyaki a kasuwa, kana da karfafa hadin kai wajen kiyaye ikon mallakar fasaha, ta yadda za su amfanawa jama'arsu baki daya. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China