in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta yi fatan za a cimma kyakkyawan sakamako a tattaunawar Sin da Amurka
2018-05-17 20:17:16 cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta yi fatan za a kai ga cimma kyakkyawan sakamako, yayin tattaunawar da wakilan kasar ta Sin ke yi da takwarorin su na Amurka, game da harkokin da suka shafi kasuwanci da cinikayya.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce akwai fatan cewa sassan biyu za su amince da juna a wasu fannoni, su kuma warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da mutunta juna.

Gao ya kara da bayyana fatan bangarorin na Sin da Amurka, za su hada gwiwa da juna, wajen ciyar da dangantakar tattalin arziki da cinikayyar su gaba.

Ya ce Sin ba ta fatan sake tabarbarewar kawance tsakanin ta da Amurka a fannin hada hadar tattalin arziki da cinikayya, sai dai kuma ta shiryawa duk wani yanayi da ka je ya zo.

Jami'in ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da fadada bude kofofin na cinikayya ga sauran kasashen duniya, ta hanyoyi madaidaita bisa ka'ida, wadanda suka yi daidai da matakinta na ci gaba. Kana hakan zai gudana a lokaci mafi dacewa da ta tsarawa kan ta, ta yadda hakan zai amfanawa al'ummar Sinawa, da ma sauran al'ummun duniya baki daya.

A ranar Talata ne dai mataimakin firaministan kasar Sin Liu He ya isa birnin Washington, domin tattaunawa da tsagin Amurka, game da batutuwa da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, bisa gayyatar da Amurkan ta yi masa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China