in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bude bikin baje kolin shirye-shiryen talibijin da fina-finai na kasa da kasa karo na 15
2018-05-17 19:06:48 cri


A yau Alhamis ne a nan Beijing, kasar Sin ta bude bikin baje kolin shirye-shiryen talibijin da fina-finai na kasa da kasa karo na 15, inda 'yan kasuwa daga kasashe da yankuna fiye da 50, suka halarta tare da yin nune-nune mabambanta. A yayin bikin, kafofin yada labaru na ketare, da masu yawon bude ido na ketare, sun ce suna mai da hankali, da maraba da shirye-shiryen talibijin da fina-finai, wadanda suka shafi al'adun kasar Sin. Wannan ne karo na farko da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG ya shirya wannan biki.
Madam Shen Jianing, babbar darektar cibiyar cinikin shirye-shiryen rediyo, talibijin da fina-finai ta kasar Sin ta yi karin bayani da cewa, an tsara wasu sabbin hanyoyi wajen yin nune-nunen shirye-shiryenmu.
"Wannan ne karo na farko da muka kebe yankunan musamman na VR, da sabbin kafofin yada labaru, da shirye-shiryen da aka fassara daga harsunan waje zuwa Sinanci, da kuma na Sinanci zuwa harsunan waje, da ofisoshin jakadancin waje da ke nan kasar Sin da dai sauransu, a kokarin samun wakilcin kasa da kasa a yayin biki na bana. Ban da haka kuma, a ganina, abun da ya fi cancanta a mai da hankali a kai shi ne, yankunan musamman guda 2 da muka kebe wa kawancen hadin gwiwa, a tsakanin kasashen da ke kan hanyar siliki ta fuskar shirye-shiryen talibijin, da kuma hadaddiyar kungiyar kamfanonin shige da ficen shirye-shiryen talibijin da fina-finai ta kasar Sin, wadda aka kafa a watan Nuwambar bara. Mun kebe wadannan yankuna 2 ne domin gwada yadda muke yayata al'adun kasar Sin a waje, da kuma gudummowar da aka bayar wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya'. "
A matsayin abokin hadin gwiwa na gamayyar hadin gwiwar kasa da kasa ta gidan talibijin na hanyar siliki, babban edita na shirin "Lokacin kasar Sin" na kafar yada labarai ta Dove Media ta kasar Burtaniya Gordon ya bayyana cewa, "Shirye-shiryen da za mu yi sun shafi kasashe da dama, wadanda suka amsa shawarar "Ziri daya da hanya daya", musamman ma kamfanonin da shirin ya shafa. Mun tsara shirye-shiryen nune-nunen harkokin kasar Sin a kasar Burtaniya, wadanda suka samu karbuwa sosai. Kuma muna fatan samar wa kasar Sin shirye-shirye na kasar Burtaniya, sabo da kasashen biyu suna sha'awar al'adun juna kwarai da gaske."
Wasu kyawawan wasannin kwaikwayo na talabijin da fina-finai, wadanda suke nuna zaman rayuwar al'ummomin Sinawa da ci gaban kasar Sin, kuma aka fassara su zuwa harsuna iri daban daban, sun fi samun karbuwa a kasashen duniya. Saurayi Redrigo Lommerte na kasar Brazil wanda ya zo kasar Sin son halartar wannan biki na nune-nunen wasannin kwaikwayo na talibijin, da fina-finai na kasar Sin ya bayyana cewa, "Ina sha'awar kallon fina-finan kasar Sin dake nuna wasan Kongfu, da yaki tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, da kuma fina-finai masu ban tsoro. Ko da yake muna da wuyar samunsu a Brazil, amma a hakika dai na fi son kallon su. Ba mu san abubuwa da yawa ba, amma idan mun kalli wasannin kwaikwayo na talibijin da fina-finai, za mu iya sanin zaman rayuwa da al'adu da kuma harsuna na kasar Sin. Idan an kalli wasannin kwaikwayo na talibijin, za a san yadda zaman al'ummar Sinawa take samun ci gaba. Ba za ka iya samun irin wannan ilmi a littafin tarihi ba." (Tasallah Yuan, Maryam Yang, Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China