in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmin Nijar sun tashi da azumi
2018-05-17 16:43:14 cri
Al'ummar musulmin Nijar ta tashi da azumin watan Ramadan din wannan shekarar 2018, bayan da aka ga jinjirin wata a wasu yankunan kasar da suka hada Diffa da Dosso. Bisa sanya idon kwamitin musulunci ne hukumomin kasar Nijar suka tabbatar da ganin watan domin baiwa al'ummar musulmin Nijar tashi da Azumi a hukumance. A cikin jawabinsa ta gidan rediyo da talabijin mallakar gwamnati, albarkacin wannan wata mai matukar falala ga 'yan uwa musulmi ne, faraminista Brigi Rafini ya maida hankali kan zaman lafiya da kuma karfafa soyayyar juna a cikin wannan lokaci, haka kuma ya bukaci 'yan Nijar su tashi tsaye tsayin daka domin gina kasarsu da ci gabanta, a cewar shugaban gwamnatin Nijar.

Maman Ada cri hausa daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China