in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Sin da Amurka su kara bude kofa ga kasashen waje
2018-05-17 13:23:53 cri

A jiya ne, aka rufe shwarwari karo na goma tsakanin shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu da tsoffin manyan jami'an Sin da Amurka a nan birnin Beijing, inda wakilan Sin da Amurka suka ganin cewa, kara bude kofa ga kasashen waje zai taimaka wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Wakilan kasar Amurka sun bayyana cewa, kara haraji kan hajoji da Amurka ta yi bai dace ba, kuma hakan zai kawo illa ga moriyar kasar Amurka kanta.

Cibiyar musanyar tattalin arzikin kasar Sin da kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Amurka sun gudanar da shawarwari karo na goma tsakanin shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu da tsoffin manyan jami'an Sin da Amurka a nan birnin Beijing tun daga ranar 15 zuwa 16 ga wannan wata, inda shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu da tsoffin manyan jami'an kasashen biyu da kuna masana da adadinsu ya kai 23 suka halarci shawarwarin, wadanda suka yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwan dake shafar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, ciki har da manufofin da ake fatan bullo da su a fannin cinikayyar Sin da Amurka, da shawarar "ziri daya da hanya daya", harkokin cinikayya ta yanar gizo, makamashi, aikin gona, masana'antu da sauransu. A yayin taron manema labaru da aka gudanar a jiya, direktan sashen Sin na kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Amurka Jeremie Waterman ya jaddada cewa, kara haraji kan hajoji da kasar Amurka ta yi zai kawo illa ga moriyar kasar Amurka. Haka kuma ya kamata a kara bude kasuwannin don warware wannan matsala, ba rufe kofa ga kasashen waje ba. Ya ce,

"Ba ma goyon bayan kara haraji kan hajoji ba, a ganinmu wannan hanya ba ta dace ba. Hanya mafi dacewa ta samun ci gaba ita ce bude kofa ga kasashen waje, ba rufe kofa ba, kana ya kamata a warware matsaloli da aka dade ana fama da su."

A shekarun baya baya nan, Sin ta gabatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje a fannonin hada-hadar kudi da sauransu. Mahalarta shawarwarin sun gano cewa, Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje, wanda hakan zai kawo moriya ga kasar Amurka. Waterman ya bayyana cewa,

"Sin tana aiwatar da shirin yin kwaskwarima da kara bude kofa ga kasashen domin samun moriyar kanta, kamfanonin Amurka su ma suna son kara samun dama a kasar Sin. A ganina, wannan zai samar da damar samun moriyar juna. A nan gaba, kamfanonin Amurka suna son sayar da kayayyaki da hidimarsu ga kasar Sin. Kana suna son yin ciniki bisa ka'idoji da dokoki cikin adalci. A fannin tattalin arziki da cinikayya, ana iya shigar da amfanin gona da iskar gas mai ruwa ruwa da sauransu daga Amurka zuwa kasar Sin, kasar Amurka za ta kara samun damar shigar da kayayyakinta zuwa kasar Sin a sauran fannoni."

A yayin shawarwarin, tsohon jakadan Sin dake kasar Amurka Zhou Wenzhong ya jaddada cewa, ba ma Sin ce take bukatar kara bude kofa ga kasashen waje ba, abin da ya kamata sauran kasashe ma su yi, yayin da suke yin hadin gwiwa tare da kasar Sin. Zhou Wenzhong ya bayyana cewa,

"Da farko shi ne kasar Sin na bukatar bunkasa tattalin arziki da zurfafa yin kwaskwarima. Ya kamata a mayar da hankali kan wani fannin hadin gwiwa yayin da ake bude kofa, wannan ba aiki ne na bangare daya kawai ba, aiki ne na hadin gwiwa. Musamman ga kasashe masu ci gaba kamar kasar Amurka, akwai bukatar su rika martaba hanyar da ta dacewa tare."

Za a gudanar da shawarwari karo na 11 tsakanin shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu da tsoffin manyan jami'an Sin da Amurka a watan Nuwanba na bana a kasar Amurka. Mataimakin shugaban majalisar cibiyar musanyar tattalin arzikin kasar Sin Wei Jianguo ya bayyana cewa, shawarwarin zai ci gaba da sa kaimi ga hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China