in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun kaddamar da wani shiri da za a ci gajiyar aikin gona zamani a Afirka
2018-05-17 10:59:57 cri

A jiya Laraba ne masana daga cibiyar nazarin aikin gona a kasashe masu zafi ta kasa sa kasa (CIAT) suka kaddamar da wani shiri da za a rika cin gajiyar aikin gona na zamani a nahiyar Afirka.

Jagoran tawagar shirin Evan Girvetz shi ne ya sanar da haka a birnin Nairobin kasar Kenya yayin taron karawa juna sani na duniya da aka bude game da dabarun sabawa da canjin yanayi a Afirka.

A karon farko shirin ya zayyana matsayi da damammaki na zuba jari da za a ci gajiyar su a bangaren noma na zamani a kasashen Afirka 14, da dabaru na kimiyya game da kudaden da shirin zai bukata wajen hasashen yanayi a nahiyar.

Sai dai kuma masanin ya ce, har yanzu galibin masu bayar da agaji da kamfanoni masu zaman kansu da gwamnatocin Afirka na ganin cewa, zuba jari a bangaren aikin noma a Afirka yana da hadarin gaske.

Yanzu dai shirin ya mayar da hankali a kasashen Senegal, da Rwanda, da Mozambique, da Uganda, da Kenya. Sauran sun hada da Tanzaniya, da Zambia, da Habasha, da Cote D'Ivoire, da Zimbabwe. Akwai kuma Lesotho, da Benin, da Jamhuriyar Nijar, da kasar Mali.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China