in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 22 sanadiyyar barkewar zazzabin lassa a Liberia
2018-05-17 10:24:30 cri
Hukumomi a Liberia, sun tabbatar da mutuar mutane 22 a fadin kasar, biyo bayan barkewar zazzabin lassa tun cikin watan Junairu.

Wata sanarwa da cibiyar kula da lafiyar al'umma ta kasar ta fitar jiya, ta ce an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar a kasar dake yammacin Afrika, inda kawo yanzu ake tsammanin mutane 81 sun kamu da ita.

Sai dai a cewar sanarwar, gwaji ya nuna cewa mutane 67 daga cikin 81n ba su kamu da cutar ba.

Kwayoyin cutar lassa ne ke haifar da cutar mai sa zazzabi da zubar jini.

Zuwa yanzu, an samu barkewar cutar a 4 daga cikin yankuna 15 na kasar, wadanda suka hada da Bong da Margibi da Nimba da kuma Montserrado.

Hukumomin lafiya na kasar, sun koka game da yawan mace macen, suna masu alakanta shi da jinkirin da marasa lafiya ke yi wajen zuwa asibiti.

Dan Adam na kamu da cutar Lassa ne, idan ya gamu da najasar bera mai dauke da cutar. Baya ga daukar matakan kariya da aka sani kamar wanke hannu a kai a kai, hukumar Lafiya ta duniya ta bada shawarar a rika ajiye kyanwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China