in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci a samar da manyan cibiyoyin binciken harkokin soja
2018-05-17 09:57:09 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada bukatar samar da sojojin da za su dace da zamani, da gina manyan cibiyoyin bincke na soja wadanda za su taimaka wajen gina rundunar soja mai karfi a sabon zamani da muke ciki.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban askarawar kasar, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar gani da ido cibiyar nazarin kimiyya a harkar soja ta kasar Sin.

Ya ce, kimiyya a harkar soja wani muhimmin bangare ne a ayyukan soja, kana jagoran duk wani canje-canje da ake fatan aiwatarwa a wannan fanni. Shugaba Xi ya ce, ya kamata duk wani bincike da za a gudanar ya dace da bukatu da yanayin ayyukan sojojin.

Shugaban na Sin ya kuma yi kira da a fito da hanyoyin da suke dacewa na hade dabaru da fasahohin kere-kere na soja, da bincike da sakamako, da ma yadda sojoji da fararen hula ke amfani da su

Xi ya ce, wajibi ne a ci gaba da karfafa biyayyar rundunar sojoji a siyasance, da kara musu karfi ta hanyar yin gyare-gyare da fasohohi na kere-kere, kana a rika kula da su kamar yadda doka ta tanada. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China