Shugaba Xi Jinping ya gana da 'yan tawagar ne a Larabar nan, karkashin jagorancin shugaban ta Pak Thae Song, wanda kuma mamba ne a hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar ta WPK, kana shi ne mataimakin shugaban kwamitin kolin jam'iyyar.
Shi ma Wang Huning, zaunannen mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, na cikin mahalarta zaman daga tsagin kasar Sin. (Saminu Hassan)