in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da Afrika na yunkurin samun kyakkyawar makoma bisa hadin gwiwa
2018-05-16 14:03:55 cri

Kimanin shekaru 5 ke nan, tun bayan da shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasar Sin da Afrika a sabon zamani, da kuma za ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne, ya gabatar da manufar, wadda ke dogaro bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin, a shekarar 2013.

Bisa wadanan tsare-tsare, Kasar Sin da Afrika, sun hada karfi da karfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, wanda ke da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba samun irinsa ba, tsakanin kasar ta nahiyar Asia da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya.

Bayan shekaru 5, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika.

Misali na baya-bayan nan shi ne, kasar Mozambique dake kudancin nahiyar Afrika, inda aka gina gada mai tsawon kilomita 187 da ta ratsa cikin teku, kana ta hade da wasu tituna, wadda kamfanin kasar Sin ya gina. Aikin da ya kawata Maputo, babban birnin kasar Mozambique.

Kamfanin gine-gine na CRBC na kasar Sin ne yake gudanar da aikin da ya lakume dala miliyan 785.8, inda kasar Sin ta samar da kaso 95 na kudin. An shirya kaddamar da gadar ne a cikin watan Yuni mai kamawa.

Gadar za ta saukaka sufuri tsakanin babban birnin da kuma garin Catembe, sannan za ta hada yankin kudancin Mozambique da kasar Afrika ta kudu, wadda ba makawa, za ta habaka cinikayya da yawon bude ido.

Manajan sashen ayyuka na kamfanin CRBC Cao Changwei, ya ce kamfanin ya samar da ayyukan yi sama da 20,000 na dindindin da na wucin gadi ga al'ummar yankin. Kuma yayin da aikin ke gab da kammaluwa, kamfanin na shirin daukar karin ma'aikata 3,800. Inda adadin Sinawa dake aiki a wurin ya tsaya kan 467.

A bangaren jin kai kuwa, kasar Sin na kula da shirin wanzar da zaman lafiya, inda take da dakaru sama da 1,000 a Sudan ta Kudu, da yakin basasar kasar ya shiga shekara ta 5. Haka zalika, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ke aikewa da ayarin jami'an kiwon lafiya zuwa kasar.

A farkon watan nan ne, mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu Martin Lumoro, ya ce likitocin kasar Sin sun bada gagarumar gudummuwa ga bangaren lafiya na kasar. Inda yake cewa "Sin, ita kadai ce kasar da ke taimaka mana. Sauran kasashe na gudun Sudan ta Kudu, amma kasar Sin tana zuwa ta taimaka mana. Ba za mu iya mantawa da irin wannan taimako ga al'ummar Sudan ta kudu ba".

Wani mai nazarin dangantakar Sin da Afrika, dake zaune a Madagascar, wato Ndrianja Ratrimoarvony, ya shaidawa kamfannin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasar Sin na samun 'karin maki' a dangantakarta da kasashen Afrika ne, saboda ba ta tsoma baki cikin harkokinsu na cikin gida, kana tana nacewa ga tsarin mutunta juna, wanda ke haifar da sakamakon moriyar juna ga bangarorin biyu.

Taron dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, wanda ya gudana a watan Disamban 2015 a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Yana aikewa da muhimmin sako ga al'ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare.

An riga an cimma galibin tsare-tsaren hadin gwiwar da aka sanar yayin taron, wadanda suka shafi harkokin masana'antu da noma da ababen more rayuwa da hada-hadar kudi da saukaka cinikayya da rage talauci da kiwon lafiya da sauransu.

Misali, zamanantar da harkokin gona, jigo ne cikin tsare-tsaren hadin gwiwar kasar Sin da Mozambique. Yayin da yake ganawa da Xinhua, Jakadan kasar Sin a Mozambique Su Jian, ya ce aikin noman shinkafa na Wanbao, dake lardin Gaza na kasar Mozambique, misali ne na hadin gwiwar Sin da Afrika. A cewarsa, "aikin zai taimakawa Mozambique sosai, wajen magance gibin shinkafa da take samu da ya kai ton 600,000 a duk shekara".

A watan Satumba mai zuwa, za a gudanar da sabon taron dandalin FOCAC a birnin Beijing, inda manyan jami'ai daga kasashen Afrika da Sin, za su tsara wasu fannonin hadin gwiwa.

Ana sa ran, kasashen Afrika da Sin za su hade manufofin da dabarunsu na samun ci gaba karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da kuma ajandar Tarayyar Afrika da ake son cimmawa zuwa 2063.

Shugaban kwamitin gudanarwa na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Zhanshu, wanda ke ziyara a kasashen Afrika 3 da suka hada da Habasha da Mozambique da Namibia tsakanin 8 da 18 na watan Mayu, ya ce "kasar Sin da Afrika, sun kasance al'umomi dake da makoma iri daya, kana suna da dadaddiyar dangantaka da kuma yunkurin samun ci gaba". (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China