in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasashen Afrika sun kammala taronsu kan shirin AfCFTA
2018-05-16 10:42:03 cri

Ministocin kudi da masana dabarun tsara manufofi na kasashen Afrika sun kammala taron karawa juna sani na kwanaki 5 a Addis Ababa na kasar Habasha, inda suka jaddada aniyarsu na amfani da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci wato AfCFTA a takaice.

Taron da ke da taken "yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci na kasashen Afrika don samar da guraben ayyukan yi da fadada hanyoyin tattalin arziki", ya tabo batutuwa masu yawa da suka hada da batun aikin gona, samar da kayayyakin more rayuwa, yaki da zambar kudade, da samar da dabarun bunkasa cigaban yankin Sahel.

Domin jaddada muhimmancin rawar da hukumomi masu zaman kansu za su bayar wajen cimma nasarar yarjejeniyar ta AfCFTA, hukumar kula da raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ta bukaci a dauki kwararan matakai cikin hadin gwiwa don habaka cigaban harkokin cinikayya a nahiyar.

Taron dai ya bukaci a samar da tsare-tsare da kuma hanyoyin zuba jari da suka dace domin bunkasa cigaban tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar.

Ministocin sun jaddada aniyarsu na yin amfani da yarjejeniyar ta AfCFTA wajen bunkasa harkokin masana'antu, da fadada hanyoyin tattalin arziki don habaka cigaban nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China