in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU tana daukar matakan dakile bullar sabuwar cutar Ebola a DRC
2018-05-16 10:18:52 cri
Cibiyar rigakafin yaduwar cututtuka ta Afrika wato (Africa CDC) tana daukar matakan da suka dace na dakile bazuwar annobar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (DRC).

A farkon makon jiya ne dai gwamnatin DRC ta ayyana bullar sabuwar cutar kwayar cutar ta Ebola (EVD) a yankin Bikoro dake lardin Equateur.

Domin mayar da martani game da sabon rahoton bullar cutar ta Ebola, cibiyar ta Africa CDC, ta sabunta shirinta na kai daukin gaggawa domin tallafawa DRC wajen shawo kan bazuwar cutar, kana cibiyar ta kira ga tagawar jami'anta da su gaggauta kai daukin gaggawa yankin da lamarin ya faru.

John Nkengasong, daraktan cibiyar ta Africa CDC, ya fada a lokacin taron manema labarai a hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika a Addis Ababa na kasar Habasha cewa, cibiyar za ta tura tagawarta a yau Laraba zuwa DRC domin su nazarci halin da ake ciki da kuma irin girman taimakon da ake bukata don tallafawa kokarin da gwamnatin DRC da sauran abokan hulda ke yi wajen dakile bazuwar annobar.

Daraktan ya ce, daga cikin mutane 20 din da cutar ta kashe a DRC, 3 ma'aikatan kiwon lafiya ne. Ya kara da cewa, cutar ta barke ne a yankin karkara na kasar, inda aka fuskanci kalubale wajen tura jami'an kiwon lafiya da kayan aikin da ake bukata zuwa yankin, lamarin da ya sa al'amura suka ta'azzara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China