in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da Ban Ki-moon
2018-05-15 20:32:47 cri

Yau Talata a nan Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugaban taron dandalin tattaunawar Asiya na Boao Mr. Ban Ki-moon.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin ba za ta rufe kofa ga kasashen waje ba, maimakon haka za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare.

Ya ce Sin za ta tsaya tsayin daka kan tafiyar da harkoki tsakanin sassa daban daban, da kiyaye tsarin ciniki a tsakanin sassa daban daban, da raya tattalin arzikin duniya wanda ke bude kofa ga kowa, da himmantuwa wajen kara bunkasa dinkuwar tattalin arzikin duniya bisa manufar bude kofa, da karbar sassa daban daban, da kawo alheri ga kowa, da samun daidaito da nasara tare.

A yayin taron shekara-shekara na dandalin da aka yi a bana, shugaba Xi ya sanar da sabbin matakan kasarsa, na kara bude kofa ga kasashen ketare bisa radin kanta. Za a aiwatar da wadannan matakai cikin hanzari, wadanda kuma za su iya kara kawo wa Asiya da ma duniya kyakkyawar damar bunkasuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China