in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya kira taron farko na kwamitin harkokin jakadanci
2018-05-15 19:25:26 cri
Yau Talata, shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin harkokin jakadanci na kwamitin tsakiyar kasar Sin Xi Jinping, ya kira, da kuma jagorantar taron farko na kwamitin harkokin jakadanci, na kwamitin tsakiyar kasar Sin, inda ya kuma ba da muhimmin jawabi.

Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya ce, akwai damammaki da kalubalolin dake gaban kasar Sin wajen neman bunkasuwa, don haka ya kamata a gane halin da kasar Sin, da ma sauran kasashen duniya suke ciki, da kuma kalubalolin dake gabammu, domin warware dukkan matsalolin da za a gamu da su, da kuma gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Ya ce a nan gaba kuma, ya kamata a zurfafa harkokin jakadanci, a tsara manyan aikace-aikacen jakadanci yadda ya kamata, da kuma karfafa tunani na fuskantar kalubaloli, domin tabbatar da ikon mulkin kasa, da tsaron kasa, da kuma ikon neman ci gaban kasar.

A sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" ya kasance muhimmin dandali, wajen inganta dunkulewar dukkanin bil Adama wuri guda. Cikin 'yan shekarun nan, an riga an samu sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, a yayin da aka ci gaba da aiwatar da wannan shiri. Don haka, ya kamata a mai da hankali kan aiwatar da sakamakon da aka cimma, a taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa na "Ziri daya da hanya daya" karo na farko, domin hada kan bangarori daban daban, da kuma habaka ayyukan bude kofa ga waje, ta yadda za a iya karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, yayin da ake ciyar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" gaba, da kuma ba da karin tallafi ga al'ummomin kasa da kasa. (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China