in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron kwalejojin Confucius na Afrika na 2018
2018-05-15 13:34:11 cri

A yammacin jiya ne, aka bude taron kwalejojin Confucius na nahiyar Afrika na shekarar 2018 a birnin Maputo, hedkwatar kasar Mozambique. Shugabannin jami'o'in Sin da kasashen Afrika 41 da aka bude kwalejojin Confucius sama da 60, da wakilai kamfanonin Sin da hukumomi kimanin 300 ne suka halarci taron, abin da ya sa girman wannan taron ya kai sabon matsayin a karon farko a tarihi.

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin Mista Li Zhanshu, bisa rakiyar shugaban majalisar dokokin kasar Mozambique, ya halarci bikin bude taron tare da yin jawabi.

A jawabinsa, shugaban jami'ar Eduardo Mondlane Orlando Antonio Quilambo ya bayyana cewa, kwalejin Confucius dake jami'arsa ta samu ci gaba sosai wajen koyar da Sinanci da taimakawa ga mu'ammalar al'adu da sha'anin ba da ilmi tsakanin kasashen biyu tun kafuwarta a shekarar 2012.

Taron na wannan karo ya kasance wani muhimmin dandali wajen kara hadin kai tsakanin kasashen biyu ta fuskar ba da ilmi.

A nasa bangare, Mista Li Zhanshu ya ce, an kafa kwalejojin Confucius sama da 500 da dakunan koyar da Sinanci 1000 ko fiye a makarantun midil ko firamare a kasashe da yankuna da suka zarce 140 a shekaru 10 da suka gabata. Wanda ya ba da gudunmawa matuka ga sha'anin habaka mu'ammalar jama'ar Sin da na kasashen waje, baya ga kara sada zumunci tsakaninsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China