in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadiyar Sin: taron dandalin FOCAC zai taimakawa raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka
2018-05-15 10:49:21 cri

Sabuwar jakadiyar kasar Sin a kasar Kenya, kana wakiliyar Sin a hukumar kare muhalli da hukumar tsugunar da mutane ta MDD, Madam Sun Baohong, ta isa birnin Nairobi, inda ta fara aiki a ranar Lahadi da ta wuce. Yayin da ake hira da Madam Sun Baohong, jakadiyar kasar Sin a kasar Kenya, ta bayyana ra'ayinta dangane da makomar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya, inda ta ce,

"Ma iya cewa huldar dake tsakanin Sin da Kenya, ta samu babban ci gaba, musamman ma cikin shekarun da suka wuce. A wajen taron koli na hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da ya gudana a bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta sun cimma ra'ayi daya, game da daukaka matsayin huldar dake tsakanin kasashen 2 zuwa abota ta hadin gwiwa a bangaren manyan tsare-tsare wadda ta shafi dukkan fannoni, ta yadda za a samar da damar kara kyautata huldar dake tsakanin Sin da Kenya a nan gaba. Bisa wannan yanayin da ake ciki ne, na zo kasar Kenya aiki, lamarin da ya sa ni farin ciki sosai. Yanzu akwai babban nauyin da aka dora min, amma duk da haka, na yi imanin cewa zan sauke nauyin yadda ya kamata. Zan yi kokari tare da abokaina na kasar Kenya, domin ciyar da huldar hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 gaba."

Madam Sun, tsohuwar jami'ar diplomasiya ce wadda ta dade tana kula da aikin hulda da kasashen dake nahiyar Afirka. A cewarta, ta gane wa idanunta yadda aka kafa dandadin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC a shekarar 2000, da yadda aka gudanar da taron kolin dandalin FOCAC a birnin Johannesberg a shekarar 2015, gami da aiwatar da sakamakon da aka samu a wajen taron. A ganinta, dandalin FOCAC wani tsari ne mai muhimmanci, wanda ya baiwa kasashen Afirka da kasar Sin damar musayar ra'ayi da hadin gwiwa a fannoni daban daban, kana taron kolin dandalin da za a gudanar da shi a birnin Beijing na kasar Sin a watan Satumban bana, zai samar da babbar gudunmowa ga kokarin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka. A cewarta,

"Taron koli na wannan karo na da muhimmanci sosai, domin zai baiwa shugabannin kasashen Afirka da na kasar Sin damar haduwa a birnin Beijing, inda za su tattauna matakan da za a dauka domin kara yaukaka huldar dake tsakanin Sin da Afirka, da kokarin samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin Sin da Afirka, da neman hanyar habaka shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Ina tsammanin wannan taron zai samar da babbar gudunmowa ga kokarin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka, gami da Sin da Kenya. Haka zalika zai amfani hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, da taimakawa wanzar da zaman lafiya a duniya, da kyautata fasahar kula da duniyarmu."

Ban da haka, jami'ar kasar Sin ta yi bayani kan yadda za a karfafa cudanyar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Kenya a fannin al'adu, inda ta ce,

"Musayar ra'ayi a fannin al'adu daya ne daga cikin manyan ginshikai 5 na huldar dake tsakanin Sin da Afirka, kana makasudin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka shi ne, neman kara fahimtar juna da kauna tsakanin al'ummomin bangarorin biyu. Yanzu haka an riga an samu nasarori a kokarin musayar al'adu tsakanin Sin da Kenya, don haka za mu kara neman ci gaba a wannan fanni a nan gaba. Za mu kammala aikin gina cibiyar nazarin kimiyya da fasaha ta hadin gwiwar Sin da Afirka, da cibiyar nuna al'adun Sin, don kara zurfafa mu'amalar da ake yi a fannin al'adu."

A karshe, Madam Sun Baohong ta ce, a matsayinta na jami'ar diplomasiya, za ta yi kokarin nuna halayya masu kyau ta matan kasar Sin, da yakinin da take da shi game da kanta, da hakuri, da kulla hulda mai kyau tare da saura, yayin da take gudanar da aikinta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China