Tarayyar Turai EU, ta sanar da tsawaita wa'adin shirinta na ba da horo a Mali da shekaru biyu, inda zai kai ranar 18 ga watan Mayu 2020.
A cewar sanarwar da tarayyar ta fitar a jiya, majalisarta ta yanke shawarar tsawaita wa'adin ne, domin ya kunshi taimakawa rundunar hadin gwiwa ta kungiyar kasashe 5 na yankin Sahel.
Majalisar ta kuma amince da ware Euro miliyan 59.7 kwatankwacin dala miliyan 71.5 ga shirin a cikin shekarun biyu.
Shirin da aka kafa a shekarar 2013, na da nufin ba da taimako da horo ga sojojin Mali, tare da ba hukumomin kasar shawarwari kan sauya tsarin rundunarta na soji.
A shekarar 2014 ne, kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Niger, suka kafa kungiyar Sahel, domin inganta hadin gwiwa a yankin, da nufin magance manyan kalubalen da suke fuskanta. (Fa'iza Mustapha)