in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala bikin baje kolin al'adun Sin inda ya samu baki mahalarta da dama
2018-05-15 10:31:43 cri

An kammala bikin baje kolin al'adu na kasar Sin karo na 14, jiya Litinin a birnin Shenzhen dake kudancin kasar, inda bikin na wannan karon, ya samu halartar baki da dama fiye da na bara.

A cewar mashirya bikin, 'yan kasuwa baki 21,386 daga kasashe da yankuna 101, adadin da ya zarce na shekarar 2017.

Bikin na kwanaki 5 ya mai da hankali kan sakamakon da aka samu cikin shekaru 40 da suka gabata wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar bude kofa da gyaran fuska a kasar Sin, da sakamakon da aka samu bayan aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya.

Filin bikin da ya mamaye muraba'in mita 105,000 ya kunshi manyan rumfuna 9 da suka mayar da hankali kan sutura da fina-finai da wallafe wallafe da al'adun gargajiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China