in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta fatattaki bata gari a yankunan dake fama da tashin hankali
2018-05-15 10:05:27 cri

Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Tukur Buratai, ya ba sojoji umarnin fatattakar bata gari daga yankin Birnin Gwarin jihar Kaduna mai fama da ayyukan bata gari cikin makonni 3.

Sama da fararen hula 100, ciki har da sojoji 11, 'yan bindiga suka kashe a kauyukan dake karamar hukumar Birnin Gwari, cikin watanni 5 da suka gabata.

Da yake kaddamar da wani sansanin soji a yankin Birnin Gwari, babban hafsan sojin, ya bukaci dakarun su tabbatar da kawo karshen kashe kashen da ake yi a yankin.

A cewarsa, ba za su sake tsayawa daukar matakan kariya ba, inda ya ce, dole ne a kaddamar da yaki. Ya ce, tun da bata garin na gudanar da ayyukansu, dole ne a mayar musu da martani kuma a murkushe su a duk inda suke. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China