in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Afirka sun yi kira da a gaggauta daukar matakan tabbatar da shirin FTA
2018-05-15 09:39:22 cri
Ministocin kudi, tsare-tsare da raya tattalin arzikin kasashen Afirka, sun yi kira da a dauki kwararan matakan ganin shirin nan na yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar (AFCFTA) ya tabbata.

Ministocin sun bayyana hakan ne yayin da suke karin haske game da shirin, a taron ministocin kasashen na Afirka karo na 51 dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Daga cikin manyan batutuwan da ministocin suka tabo yayin taron, har da yadda za a aiwatar da gyare-gyare ta yadda kasashe mambobi za su ci gajiyar shirin, da daukar matakan da suka dace na karfafa yin takara, da batutuwan da suka shafi haraji da muhimmancin yin hadin gwiwa da kasashen duniya a wannan fanni.

Karamin sakataren kasafin kudi na kasar Angola Alia-Eza Nacilla Gomes Da Silva, yana ganin cewa yin cinikayya ba tare da shamaki ba, ba kawai yana nufin kasancewa tare ba. Batu ne da ya shafi canja tsare-tsare, da fito da manufofi na bai daya da tsara ajandodin da ba su ci karo da na kasa da kasa ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China