Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin babban yankin kasar da yankin musamman na kasar Hong Kong domin raya ci gaban kimiyya da fasaha, inda ya lashi takobin tallafawa yankin don zama cibiyar bunkasa fasahar kirkire kirkire ta kasa da kasa, da kuma baiwa masana kimiyya na yankin damar ba da gudumowarsu wajen ci gaban kasa ta fannin kim'iyya da fasaha.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin aikin sojin kasar Sin, ya ba da wannan muhimmin umarni ne a daidai lokacin da yake mai da martani dangane da wasikar da wasu 'yan kimiyya 24 dake yankin Hong Kong na kasar suka rubuta masa a watan Yunin shekarar 2017.(Ahmad Fagam)