in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya taya al'ummar Iraqi murnar gudanar da zabe
2018-05-14 10:17:20 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya taya al'ummar kasar Iraqi murnar gudanar da zaben majalisar dokokin kasar, kakakin babban sakataren Stephane Dujarric shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce, bayan nasarar da dakarun sojojin kasar Iraqin suka samu wajen fatattakar mayakan kungiyar IS, zaben na ranar Asabar zai sake tabbatar da ci gaban mulkin demokaradiyyar a Iraqin.

Guterres ya yabawa jajurcewar da jami'an hukumar zaben kasar suka yi, da kokarin da wakilan jam'iyyu da kuma jami'an tsaron kasar suka yi wajen shirya zaben cikin lumana da kwanciyar hankali. Kana ya yabawa dukkan bangarorin Iraqin da suka taka rawa wajen shirya zaben, musamman mutanen dake zaune a sansanonin 'yan gudun hijira wadanda suka jefa kuri'unsu, duk da irin matsanancin halin rayuwa da suke ciki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China