in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta yi kira da a taimakawa wadanda ake nunawa banbanci
2018-05-11 16:41:30 cri
Kafar yada labarai ta kasar Afrika ta kudu, ta ba da labari a jiya 10 ga wata cewa, majalisar ministocin kasar ta yi kira ga al'ummar kasar da su dauki matakai, na kawar da bambancin jinsi, sakamakon bambancin da ake kara nunawa mata da yara.

A gun taron da majalisar ministocin Afrika ta kudu ta yi a wannan rana, ministan zirga-zirga Mokonyane ta bayyana cewa, ya kamata ko wane dan kasar Afrika ta kudu, ya sauke nauyin dake wuyansa na tabbatar da hakkin mata da yara na samun ilimi, da kuma yin amfani da ko wane tsari, don taimakawa wadanda suke fama da wariya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China