in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya ziyarci garin Yingxiu a gabanin ranar cika shekaru goma da aukuwar girgizar kasa ta Wenchuan
2018-05-11 10:58:43 cri

A ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2008, girgizar kasa mai tsanani matuka ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Ba da dadewa ba bayan aukuwar masifar, mataimakin shugaban kasar Sin a wancan lokaci Xi Jinping ya ziyarci wurin domin ba da jagoranci kan aikin ceto. Yanzu haka bayan sake ginin yankin a cikin shekaru goma da suka gabata, ko a wane irin hali mazauna gundumar Wenchuan suke?

Shugaba Xi yana mai da hankali sosai kan rayuwarsu, a don haka ya sake ziyartar garin Yingxiu na gundumar Wenchuan, inda aka yi fama da girgizar kasa mafi tsanani a watan Fabrairun bana.

A safiyar ranar 12 ga watan Fabrairun bana, shugaba Xi Jinping ya isa wurin da makarantar midil ta Xuankou take a baya, inda ya ajiye kwandon furanni domin nuna alhininsa ga 'yan uwa Sinawa wadanda suka rasa rayukansu a yayin girgizar kasar, da jaruman da suka sadaukar da rayukansu yayin aikin ceton jama'ar da masifar girgizar kasar ta rutsa da su, kuma ya yi sujada har sau uku.

A gaban ginin ajin makarantar midil ta Xuankou, akwai wani agogo mai girma wanda ke nuna lokacin aukuwar girgizar kasar kafin shekaru goma da suka gabata wato karfe 2 da mintoci 28 na yamma, a kusa da agogon, an kafa wani bango, inda aka rubuta babbar hasarar da aka gamu da ita, haka kuma an rubuta ayyukan ceton da daukacin jama'ar kasar suka gudana, a karkashin jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Shugaba Xi ya jaddada cewa, dole ne a kiyaye wurin yadda ya kamata, zai kasance muhimmin sansanin yada manufar kishin kasa.

Har kullum shugaba Xi yana mai da hankali kan rayuwar jama'ar gundumar Wenchuan tun bayan aukuwar girgizar kasa, yanzu ma ya sake zuwa wurin, ya tambayi mazauna yankin halin da suke ciki bayan sake ginin yankin, ga hirarsu,Shugaba Xi ya tambaye su cewa, yanzu gine-ginen makarantar suna iya jure girgizar kasa mai karfin maki nawa? Wani ma'aikacin hukumar dake lura da aiki ya amsa da cewa, yanzu gine-ginen jama'a suna iya jurewa girgizar kasa mai karfin maki 9, kuma gidajen kwana suna iya jurewa maki 8 na girgizar kasa. Shugaba Xi ya jaddada cewa, babban sakamakon da aka samu bayan aukuwar girgizar kasar mai tsanani ya nuna cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana ba da jagoranci mai karfi, haka kuma ya nuna cewa, tsarin gurguzu na kasar Sin yana da inganci, kuma nan gaba za a ci gaba da sanya kokari, domin kara kyautata rayuwar jama'a.

Garin Yingxiu yana kudu maso gabashin gundumar Wenchuan, kuma mutane sama da dubu 16 ne a garin suka rasa rayukan su yayin girgizar kasar, adadin da ya kai kaso 1 bisa 3 na daukacin mazaunan garin. Kana hasarar tattalin arzikin da garin ya gamu da ita kai tsaye ta kai kudin Sin yuan biliyan 4 da miliyan 500. Yanzu an kusa sabunta garin bayan sake ginin sa. Kantuna da dama sun bude kofa a gefuna biyu na tituna, domin maraba da zuwan masu sayayya. Jiang Weiming, ya bude wani kantin samar da shayi a wurin, shi da iyalansa sun gayyaci shugaba Xi zuwa kantinsu domin ziyara, ga hirarsu, Shugaba Xi ya tambaye shi cewa, "Ko suna samun shayin ne a garinsu?"

Mai kanti ya ba da amsa cewa, "E haka ne, an kafa kamfanin samar da shayi ne kafin aukuwar girgizar kasar ta shekarar 2008, daga baya mun sake farfado da aikin sa ne kawai."

Hakika garin Yingxiu yana da dogon tarihin samar da shayi, adadin itatuwan shayi wadanda shekarunsu suka kai 100 ya kai sama da dubu 200. A shekarar 2017, shayin da kantin Jiang Weiming ya samar ya taba samun damar zuwa kasashe sama da dari daya domin baje koli, yayin wani bikin da kungiyar sada zumunta dake tsakanin kasar Sin da kasashen waje ta kasar Sin ta shirya, domin yada manufa game da sakamakon da aka samu bayan da aka aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Shugaba Xi ya yaba da kokarin da suke yi, inda ya yi fatan za su kara taka rawar gani kan aikin gini yankin bisa shawarar "ziri daya da hanya daya."

Yanzu garin Yingxiu yana samar da hidimar yawon bude ido a kauyuka, masu yawon shakatawa da suke zuwa wurin sun karu sannu a hankali. Gaba daya adadin dakunan cin abinci, da dakunan kwana a garin ya riga ya kai sama da dari daya.

Da mazauna suka ga shugaba Xi ya zo garinsu, sai fita domin gaida shi. Shugaba Xi, ya ce yana fatan za su ci gaba da jin dadin rayuwarsu bayan kokarin da suka yi, a cewarsa,"Ina begen wurin matuka, bayan shekaru goma da suka wuce, na ga sauye-sauye da suka faru a nan."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China