Singapore na farin cikin zama wurin da shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka za su yi ganawa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Singapore ta fitar da wata sanarwa jiya Alhamis, inda ta ce, kasar na farin-cikin ganin cewa, ta zama wurin da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da takwaransa na Amurka Donald Trump za su yi ganawa. A cewar sanarwar, Singapore na sa ran ganawarsu a wannan karo za ta taimaka ga shimfida zaman lafiya a zirin Koriya.
Tun a ranar Alhamis, Trump ya sanar ta shafinsa na sada zumunta cewa, zai gana da Kim Jong-un a Singapore a ranar 12 ga watan Yunin bana. Ya kuma ce, yana fatan ganawarsu za ta zama wani lokaci na musamman ga yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a duk fadin duniya.(Murtala Zhang)