in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta samar da tallafin jin-kai ga Somaliya
2018-05-10 20:28:12 cri
Yau Alhamis, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, gwamnatin kasar ta kuduri aniyar samar wa gwamnatin Somaliya tallafin jin-kai na gaggawa, don taimaka mata yaki da bala'in ambaliyar ruwa.

A 'yan kwanakin nan ne ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa mummunan ambaliyar ruwa a kasar ta Somaliya, inda matsalar ta rutsa da mutane sama da dubu dari hudu.

Mista Geng ya bayyana cewa, kasar Sin na jajantawa dimbin mutanen da ambaliyar ruwar Somaliyar ta tilasta musu barin muhallansu. Gwamnatin kasar Sin za ci gaba ta sanya ido kan halin da ake ciki a Somaliya, da samar da tallafi da goyon-bayan da Somaliya take bukata daidai karfinta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China