in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta lalata galibin makamai masu linzamin da Isra'ila ta harba mata
2018-05-10 20:24:57 cri

Rahotanni daga kasar Syria na cewa, makaman tsaron sararin samaniyar kasar sun mayar da martani kan makamai masu linzamin da kasar Isra'ila ta harba kan cibiyoyi sojojin kasar da sanyin safiyar yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria(SANA) ya ruwaito sojojin kasar na cewa, makamai masu linzami sun lalata tashar sarrafa makamai, da rumbon adana makamai, sannan sun lalata bataliyoyin tsaron sararin samamiyar kasar, baya ga sojoji uku da suka mutu, biyu kuma suka jikkata.

Wata sanarwa da sojojin kasar ta Syria suka fitar, ta ce wannan takala, za ta kara karfafawa sojojin gwiwar kara samun nasara a fafatawar da suke yi da kungiyoyin 'yan ta'adda a sassan kasar.

A hannu guda kuma, wata sanarwa da dakarun tsaron Isra'ila(IDF) suka fitar, ta bayyana cewa, jiragen saman yakin kasar sun kai gomman hari kan cibiyoyin sojan Iran dake Syria da sanyin safiyar yau, domin mayar da mayar kan harin makamin rokar da dakarun juyin juya halin Iran din suka kai kan yankunan tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China