in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci taron shugabannin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 7
2018-05-10 10:54:02 cri
Da sanyin safiyar ranar Laraba 9 ga watan nan ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang, da firaministan kasar Japan Shinzo Abe, da shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, sun halarci taron shugabannin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 7, tare da ganawa da 'yan jarida tare.

Li Keqiang ya jaddada cewa, kara hadin gwiwa dake tsakanin kasashen uku, shi ne bukatun raya kasashen uku, da kuma begen sauran kasashen dake yankin da kuma kasa da kasa baki daya. Ya ce ya kamata kasashen uku su rike dama, da fadada hadin gwiwarsu ta samun moriyar juna, da sa kaimi ga samun zaman lafiya da wadata tare a yankin.

Bayan shekaru biyu da rabi, an sake gudanar da taron shugabannin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu a birnin Tokyo dake kasar Japan a ranar 9 ga wata. Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi nuni a cikin jawabinsa cewa, a matsayin manyan kasashen tattalin arziki a duniya, kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu su ne muhimman abokan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, wadanda suka dauki nauyinsu na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin, da gudanar da tsarin raya yankin na bai daya, da tabbatar da zaman lafiya da lumana a yankin. Li Keqiang ya bayyana cewa,

"Gudanar da taron shugabannin kasashen Sin, da Japan da Koriya ta Kudu ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga raya dangantakarsu. Domin moriya iri daya ta kasashen uku ta zarce matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu. Ta wannan taro, za a iya fadada moriyarmu ta bai daya, da kuma warware matsaloli. Tabbatar da tsarin gudanar da wannan taro a kullum zai taka muhimmiyar rawa wajen bada jagoranci."

Li Keqiang ya ce, ya kamata kasashen uku su tabbatar da yin ciniki cikin 'yanci, da sa kaimi ga raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya. Kana su tabbatar da tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban bisa ka'idoji, da kin amincewa da ra'ayin bada kariya ga cinikayya. A sa kaimi ga raya tsarin tattalin arzikin nahiyar Asiya mai bude kofa ga kasashen waje da hadin gwiwa da kuma daidaici. Li Keqiang ya ce,

"Ya kamata bangarorin uku su gaggauta yin shawarwari kan yankin yin ciniki cikin 'yanci, da sa kaimi ga yin shawarwari na raya dangantakar abokantaka ta tattalin arziki a dukkan fannoni wato RCEP, don nuna goyon baya ga yin ciniki cikin 'yanci. Kana ana iya kara bude kofa ga juna don maida kasashen uku matsayin muhimman kasuwani na juna, da kuma kara hadin gwiwa tare da sauran kasashe, don samun bunkasuwa tare."

Game da halin zirin Koriya da aka samu babban canji, Li Keqiang ya yi nuni da cewa, ana maraba da sake komawa hanyar yin shawarwari kan batun nukiliya na zirin Koriya. Ya kuma taya murnar ganawa tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da ta Kudu, tare da fatan za a yi ganawa a tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka. Ya ce,  

"Ana fatan bangarori daban daban za su rike damar su, da sa kaimin gudanar da shawarwari don warware batun zirin Koriya ta hanyar siyasa, da cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin, da kokarin samun zaman lafiya mai dorewa. Kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa kan wannan batu."

A nasu bangare, firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa, kasashen uku sun nuna goyon baya ga yin ciniki cikin 'yanci, da bude kasuwanninsu ga juna. Japan ta yaba da kokarin da kasar Sin ta yi wajen warware batun zirin Koriya. Ya kamata Japan da Sin da Koriya ta Kudu su kara yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa, don sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya.

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya bayyana cewa, kasashen Sin da Japan sun tsaya tsayin daka kan kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya, da nuna goyon baya ga yin shawarwari tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu, wanda ya sa kaimi ga gudanar da shawarwari tsakanin kasashen uku cikin nasara. Sin da Japan sun taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin samun zaman lafiya a zirin Koriya. Babu shakka za a samu zaman lafiya da wadata a zirin Koriya, da yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya. Ya kamata kasashen uku su fadada hadin gwiwarsu a fannonin kiyaye muhalli, da kiwon lafiya, da makamashi, da yaki da bala'u dake shafar zaman rayuwar jama'a, don amfanin jama'arsu. (Zainab Zhang)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China