in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta ce janye tallafin Amurka ba zai warware rikicin kasar ba
2018-05-10 09:29:59 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta kudu Mawen Makol Arik, ya ce kudurin da Amurka ke yi na janye tallafin da take baiwa Sudan ta kudu, ba zai taimaka wajen kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar kasar ba.

Mr. Arik, ya ce janye tallafin zai shafi yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya, duba da cewa, hakan zai sanyaya gwiwar sassan masu ruwa da tsaki game da batun rungumar shawarwari.

A ranar Talata ne dai gwamnatin Amurka ta yi barazanar janye tallafin da take baiwa Sudan ta kudu, sakamakon fadace fadace dake ci gaba da wakana a kasar, tana mai cewa, gwamnatin shugaba Salva Kiir ta rasa kimar ta a idanun duniya.

Kaza lika Washington ta soki rundunar sojan Sudan ta kudu da farwa 'yan adawa, da kuma batun zabe kasar da har yanzu ke cikin wani yanayi na rashin tabbas.

To sai dai kuma Mr. Arik ya ce, ba wata kasa guda dake da ikon auna kimar Sudan ta kudu. Jami'in ya ce, gwamnatin su na fatan ci gaba da tattaunawa da tsagin Amurka, a wani mataki na lalubo hanyoyin kawo karshen dambarwar siyasar kasar.

Sudan ta kudu dai ta tsunduma yakin basasa tun daga karshen shekarar 2013, lamarin da ya haifar da mummunan yanayin kwararar 'yan gudun hijira. MDD ta kiyasta cewa, 'yan kasar kusan miliyan 4 ne suka rasa matsugunnan su, inda wasu ke samun mafaka a cikin kasar, yayin da wasu da dama kuma suka fantsama sauran kasashe makwafta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China