in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya taya Medvedev murnar yin tazarce
2018-05-09 10:46:31 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya taya takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev, murnar cimma nasarar ci gaba da mulkinsa.

Mista Li Keqiang, wanda ya bugawa takwaran nasa na Rasha waya a jiya, ya ce dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu, na samun bunkasuwa cikin sauri a shekarun baya-baya nan. Baya ga haka, suna samun ci gaba sosai game da hadin gwiwarsu a wasu fannoni, ciki hadda ciniki, zuba jari, makamashi, sha'anin gona, zirga-zirgar sararin samaniya, al'adu da dai sauransu, abin da ya sa kaimi ga bunkasuwar kasashen biyu baki daya. A cewar Mista Li, yana fatan hadin gwiwa da Mista Medvedev don kara daga dangantakar dake tsakanin kasashensu zuwa sabon matsayi, da kara ba da gudunmawa wajen hadin gwiwa a dukannin fannoni nan gaba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China