in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 58 sun mutu a sanadin harin da aka kai wa kauyen Gwaskwa
2018-05-08 10:30:57 cri
Sarkin kauyen Gwaska da aka kai wa hari, a jihar Kaduna dake arewa maso tsakiyar Nijeriiya, ya tabbatar da cewa, mutanen da suka mutu sanadin harin sun karu zuwa 58.

Zubairu Mai Gwari, ya fadi haka ne a jiya Litinin, inda ya ce, tuni jami'an tsaro suka gano gawarwakin 58, sai dai akwai wasu da dama da suka bace.

Da yammacin ranar 5 ga wata ne, wasu dakarun da ba a san ko su waye ba, suka kutsa cikin kauyen Gwaska da ke yankin Birnin-Gwarin jihar Kaduna, inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane tare da jikkatar wasu da dama. Dakarun sun kuma kona gidaje da dama a kauyen mai mazauna kimanin 3000.

Kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa, har yanzu ba a kama wadanda suka aikata laifin ba, amma ana ci gaba da kokari.

Baya ga haka, gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya fitar da sanarwar cewa, za a jibge wata rundunar soja ta dindindin a yankin Birnin-Gwari, don magance karin aukuwar makamancin al'amuran.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China