in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya nada Medevedev matsayin sabon firaministan kasar Rasha
2018-05-08 10:06:42 cri

Shafin yanar gizo ta Intanet na fadar shugaban kasar Rasha ya ruwaito a jiya cewa, shugaban kasar Vladimir Putin, ya gabatarwa majalisar wakilan kasar Dimitry Medvedev a matsayin sabon faraministan gwamnatin Rasha.

Bisa kundin tsarin mulkin Rasha, wannan nadi na bukatar amincewar majalisar wakilai. Rahotanni daga kafar yada labarai ta kasar na cewa, an tarwatsa tsohuwar gwamnati bayan Putin ya yi rantsuwar kama aiki a sabon zagaye, kuma Medvedev zai gudanar da aikinsa a matsayin mukadashin firaminista kafin a kafa sabuwar gwamnati, wadda za a yi bayan mako guda da nada sabon firaminista.

Majalisar wakilan kasar dake kunshe da mambobin jam'iyyu hudu mafi girma, za ta tattauna kan sabon firaministan a yau 8 ga wata. Bisa kundin mulkin kasar, za a amince da wanda aka gabatar da shi gaban majalisar ne bayan ya samu kuri'un amincewa 226 daga cikin 450.

An ce, Medvedev ya fara wa'adinsa na firaministan kasar ne daga ranar 8 ga watan Mayun shekarar 2012. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China