Rundunar Sojan Nigeria, ta ce dakarunta sun gudanar da ayyukan ceto sau da dama a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeria, inda suka kubutar da mutane kimanin dubu daya daga hannun kungiyar Boko Haram.
Kakakin rundunar ya ce, sojojin hadin gwiwa na Kamaru da Chadi da Niger da Nigeria ne suka gudanar da wadannan ayyuka a kwanakin baya.
Sojojin sun kuma harbe mambobi biyar na Boko Haram yayin ayyukan da suka gudanar cikin watan da ya gabata a jihar Borno, inda kuma suka ceto mutane 149.
Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar ta kaddamar da ayyukan soja na dakile Boko Haram dake boye a jihar Borno sau da dama a bara. (Amina Xu)