in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga Amurka da ta karfafa hada kai da Sin dake tasowa
2018-05-07 13:19:49 cri

Kungiyar "The Committee of 100" ta kasar Amurka ta shirya taronta na shekara-shekara na bana a tsakanin raneku 5 da 6 ga wata, a Santa Clara na lardin California na kasar Amurka. Taron da ya samu halartar kwararru kimanin 500 a fannonin siyasa, tattalin arziki, masana'antu, fasahohi da dai sauransu daga kasashen Sin da Amurka, inda suka tattauna kan yadda dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka take a yanzu haka, da kiyaye ikon mallakar fasaha, bunkasuwar fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam, da mu'amala tsakanin Sinawa Amurkawa, da kuma sauran muhimman batutuwa.

An kafa kungiyar "The Committee of 100" mai hedkwatarta a birnin New York na kasar Amurka ne a shekarar 1990. Kungiyar ta hada kwararru Sinawa dake Amurka a fannoni daban daban, dake da nufin raya dangantaka tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Amurka. An sanya kungiyar cikin jerin kungiyoyin Sinawa da suka fi karfi a kasar Amurka. A yayin taronta na bana, mahalarta sun bayyana cewa, dole ne Amurka ta yi kokarin hada kai da kasar Sin dake tasowa, kana da kara zuba jari kan fannonin yin kirkire-kirkire da ba da ilmi da dai sauransu, don cimma burin samun moriyar juna tare.

A matsayinsu na kasashe biyu da suka fi girma a fannin tattalin arziki a duniya, rikicin cinikayya dake kasancewa tsakanin kasashensu na jawo hankulan duk duniya sosai, wannan dai, ya kasance muhimmin batun da aka tattauna a taron na kungiyar "The Committee of 100". Masani mai kaifin basira na Amurka, kuma babban mai nazari na asusun wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa na Carnegie, Yukon Huang yana ganin cewa, ko da yake matsalar dake tsakanin kasashen biyu ta bullo ne ta hanyar rikicin cinikayya, amma a hakika dai an haifar da matsalar ne sakamakon ra'ayin takara da kasar Amurka ke nunawa kan tasowar kasar Sin.

"Me ya sa kasashen yamma ke damuwa sosai da tasowar kasar Sin a matsayin muhimmiyar kasa a fannin cinikayya? Domin kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen fitar da kayayyakin sana'ar kire-kire a cikin shekaru 10 zuwa 15 da suka gabata, hakan ya sa ta kasance babbar kasa dake gaba a fannin, amma a cikin wannan lokaci, ko wace kasa dake kungiyar G7 dake kunshe da muhimman kasashe a fannin masana'antu sun ja baya a fannin."

Binciken da kamfanin ba da shawarwari na Gallop ya yi ya nuna cewa, kafin shekaru 15 da suka gabata, yawancin mutanen Amurka suna tsamanin kasarsu ce babbar kasa a fannin tattalin arziki. Amma, bayan matsalar kudi da ta faru a shekarar 2008, yawancinsu suna ganin cewa, kasar Sin ce babbar kasa mai karfi a fannin tattalin arziki. Baya ga haka, wasu mutanen Amurka sun yi imanin cewa, an samu babban gibi dake akwai a kasar su ne sakamakon rarar kudi da Sin ta samu a fannin cinikayya. Amma, a hakika dai an yi haka ne saboda ainihin cinikayya na kasashen biyu.

Babban mai nazari na sashen nazarin harkokin kasa da kasa da na jama'a na Watson na jami'ar Brown ta kasar Amurka, Chas W. Freeman, Jr ya nuna cewa, kasar Amurka ta zargi manufofin masana'antu na sauran kasashe a yayin da take fuskantar matsalolinta, ciki har da gibin cinikayya, kuma ta yi barazanar karbar kudin harajin kwastan domin yanke hukunci, musammam saboda ci gaban da sauran kasashe suka samu, inda ya ce wannan abu ne na rashin hankali.

"Har zuwa yanzu, manufofin masana'antu da ba da kudin tallafi na karbar haraji suna kasancewa muhimman abubuwa na inganta ci gaban tattalin arzikin kasashen Faransa, da Jamus, da Japan da kuma Koriya ta kudu. Babu amfani idan an zargi kasashen waje da yin amfani da wadannan manufofi, kuma hakan ba zai taimake mu wajen samun ci gaba ba. Idan muna fatan canja hanyar da suke bi, to dole ne mu ma mu canja hanyar da muke bi."

A nasa bangaren, tsohon jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Gary Faye Locke ya bayyana cewa, kamata ya yi kasar Amurka ta kara zuba jari kan yin kirkire-kirkire da ba da ilmi a kasarta.

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne, yadda Amurka za ta kara matsayinta a fannonin fasahohin zamani da na kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam. A shekarar 2015, kason kudin da gwamnatin kasar Amurka ta biya wajen nazari da habaka bisa na GDP ya kai kashi 1 cikin 3 bisa na shekarar 1964. Shirin kasafin kudi da shugaba Trump ya gabatar, ya ce, ya zuwa shekarar 2028, kudin da za a biya ba domin tsaron kasa ba zai ragu da kashi 42 cikin dari, ciki har da a fannin nazarin kimiyya. Idan kasar Amurka ba ta son kara zuba jari kan kimiyya da fasaha, ba za ta kiyaye matsayinta na jigo a fannin kirkire-kirkire ba, tun da ta kara karbar kudin haraji daga kasar Sin da daukar sauran wasu matakai." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China