in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Korea ta arewa ta zargi Amurka da son sake tsananta halin da ake ciki a zirin Koriya
2018-05-07 11:51:56 cri

Kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Korea ta arewa, ya bayyana a jiya cewa, jerin matakan da Amurka ke dauka na matsin lamba kan kasar na nufin tsananta halin da zirin Korea ke ciki yanzu.

Rahotanni daga Korea ta arewa na cewa, kakakin ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa game da matakan kara sanya takunkumi da Amurka ke dauka kan kasar. Kakakin ya ce, a kwanankin baya, Amurka ta watsa bayanai bisa kuskure, inda ta ce shawarwarin da aka yanke na kawar da makaman nukiliya a zirin Korea da bangarorin Koriya biyu, wato Koriya ta arewa da ta kudu suka cimma cikin sanarwar Panmonjom, ta kasance sakamakon takunkumin da Amurkar ta kakkabawa Koriya ta arewa.

Ya ce, Amurka na bayyana matsayin da take dauka, na nacewa ga kara matsawa kasar Koriya ta arewa lamba, tare da jibge sansanonin soji a zirin Korea, don Korea ta arewa ta yi watsi da makamanta na nukiliya baki daya. Ban da wannan kuma, Amurka ta kan mai da hankali kan batun hakkin bil Adam sosai da nufin kara tsananta halin da zirin ke ciki.

Hakazalika, kakakin ya ce, ba za a iya warware batun zirin Koriya ba idan Amurka ta dauka cewa, niyyar Koriya ta Arewa na shimfida zaman lafiya, ta kasance tamkar tsoro, don kaucewa ci gaba da matsa mata lamba da kakaba takunkumi da Amurkar ke yi. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China