in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar AU ta isa Sudan don nazarin yanayin tsaro da na 'yan gudun hijira
2018-05-07 10:49:15 cri

Tawagar tarayyar Afrika AU, ta isa Sudan don nazarin ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya da kuma halin da 'yan gudun hijira ke ciki a kasar.

Wata sanarwa da AU ta fitar a jiya Lahadi, ta ce kwamitinta na sulhu PSC, ya fara ziyarar yini 5 a ranar Asabar da ta gabata a yankunan Khartoum da Darfur domin nazarin.

Kwamitin zai yi nazarin ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin tarayyar Afrika da MDD wato UNAMID, la'akari da aikin nazarin shirin da ake a yanzu, wanda ke da nufin duba yiwuwar janye shi daga kasar.

Har ila yau, kwamitin zai kuma bukaci bangarorin Sudan su mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hnkali a Darfur, biyo bayan warware rikicin da ya shafe kusan shekaru 15.

Sanarwar ta ce, ziyarar ta kwamitin PSC na zuwa ne, a daidai lokacin da aka samu ingantuwar yanayin tsaro, wanda ke bukatar janye shirin UNAMID a hankali. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China