A kwanakin baya ne, Amurka ta fitar da wata sanarwa, inda ta soki gwamnatin kasar Sin, saboda ta bukaci kamfanonin kasashen waje dake aiki a kasar, su kaucewa ayyana yankunan Hongkong da Macau a matsayin 'kasa' a shafukansu na Intanet gami da litattafansu na talla.
Game da zargin ne Mista Geng Shuang ya yi sharhi a jiya, yana mai cewa, duk abun da Amurka za ta fada, sam ba zai canja gaskiyar magana ba, wato kasancewar kasar Sin daya tak a duk fadin duniya, kana, Hongkong da Macau, yankuna ne da ba za'a iya balle su daga kasar Sin ba.
Geng ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da raya dangantakar abota da sauran kasashen duniya, bisa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Geng ya sake nanata cewa, kamata ya yi kamfanoin kasashen waje dake kasar Sin, su girmama cikakken yankin kasar, tare da mutunta dokokin kasar da al'ummarta baki daya. (Murtala Zhang)