Ban da haka, cikin sanarwar hadin gwiwa da aka gabatar bayan taron, an yi kira da a yi hattara wajen tunkarar matsalar da ka iya bullowa ta koma bayan tattalin arzikin duniya. Sanarwar ta kara da cewa, kowa ya lura da hadarin dake tare da matakan kariyar ciniki, inda kasashe daban daban ke daga matsayin ruwan da ake bayarwa bisa ajiyar kudi, sannan saurin karuwar kudin ruwa ya zarce yadda aka yi hasashe. Ban da haka kuma, ana ci gaba da fuskantar rikicin siyasa a wasu shiyyoyi.
Ganin yanayin da ake ciki, ya sa mahalarta taron jaddada kin amincewa da duk wani mataki irin na kariyar cinikayya, da bukatar bude kofa domin gudanar da ciniki da zuba jari, da karfafa musayar ra'ayin da ake yi tsakanin kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu.(Bello Wang)