in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Warren Buffett: Huldar dake tsakanin Sin da Amurka za ta iya amfanawa kasashen 2
2018-05-06 15:47:06 cri
Shahararren dan kasuwar Amurka Warren Buffett ya ce, kasashen Amurka da Sin, suna da tattalin arziki mafi girma a duniya, kana huldar dake tsakanin kasashen 2 za ta iya amfana musu baki daya. Mista Buffett ya bayyana haka ne lokacin da yake halartar taron masu hannayen jarin kamfanin inshora na Berkshire Hathaway da ya gudana a birnin Omaha dake jihar Nebraskar kasar Amukra, a jiya Asabar. A cewar Buffett, nan da wani lokaci mai tsawo, kasashen Amurka da Sin za su ci gaba da kasancewa manyan kasashen dake yin tasiri ga tattalin arzikin duniya da sauran fannoni, kana suna da moriyar bai daya kan batutuwa daban daban. Ya ce la’akari da karfin tattalin arzikinsu, kasashen Amurka da Sin, za su iya amfanawa juna da samun moriya tare. Haka zalika, Mista Buffett ya kara da cewa, yadda ake gudanar da ciniki cikin ‘yanci na da alfanu sosai, haka kuma zai taimakawa ci gaban al’ummun duniya. Har ila yau, yayin taron dandalin masu zuba jari na kasashen Amurka da Sin da ya gudana a birnin Omaha a ranar Jumma’a, mista Buffett ya ce, yadda tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin shekaru gomai da suka wuce, wani abu ne mai ban mamaki, al’amarin da ya sa shi nuna niyyarsa ta kara zuba jari ga kasuwannin kasar Sin.(Bello)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China