Saboda haka ne, mahalarta taron suka nuna cewa, akwai bukatar sabon tsarin raya sha'anin gona, matakan da za a dauka suna kunshe da kara samar da abinci da hanyar dogaro da hukumomi masu zaman kansu da sa kaimi ga aikin kirkire-kirkire. Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu, matsakaicin shekarun haifuwar manoman Nigeria ya kai 65, hakan ya sa tilas ne a shigo da wasu matasa cikin wannan sha'ani nan gaba. Ban da wannan kuma, gwamnati ta rage kudin ruwa da ake biya a fannin aikin gona zuwa kashi 5 bisa dari, idan ba haka ba sha'anin gona a kasar ba zai ci gaba ba ko kadan. Dadin dadawa, shigo da jarin kasashen waje da kara hadin gwiwa da kasashen waje don fitar da amfanin gona masu inganci da kuma rage kalubalolin da za a fuskanta wajen bunkasa sha'anin gona bisa sabbin tsare-tsare na yin kirkire-kirkire da kwaskwarima don biyan bukatun hatsi, saboda tabbatar da samar da isasshen abinci ita ce hanyar da ta dace wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin Nigeria. (Amina Xu)