in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan 'yan jaridun da aka kashe a 2018 ya karu da kaso 57
2018-05-03 10:40:41 cri

Kungiyar dake rajin kare hakkin 'yan jaridu dake birnin Geneva (PEC) ta bayyana a jiya Laraba cewa, yawan 'yan jaridun da aka kashe cikin watanni hudu na farkon shekarar 2018 da muke ciki a kasashe 18 ya karu zuwa 44, sabanin 28 a makamin lokaci na bara.

Yayin da ake bikin ranar 'yancin manema labarai ta duniya yau Alhamis uku ga watan Mayun shekarar 2018, PEC ta ce, ta damu matuka da yadda ake kashe 'yan jaridu a duniya. Ta ce, daga watan Janairu zuwa Afrilun wannan shekara, yawan 'yan jaridun da aka kashe ya karu da kaso 57 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gaba ce ta.

Haka kuma kungiyar ta PEC ta ce, ta kadu game da kisan 'yan jaridu 9 yayin da wasu bama-bamai biyu da suka tashi a Kabul, babban birnin Afghanistan a ranar 30 ga watan Afrilu, inda ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan yadda wani 'dan kunar bakin wake ya yi badda kama a matsayin mai daukar hoto ya tayar da bam din dake jikinsa a cikin cunkoson jama'a, ya kuma hallaka manema labarai.

Kungiyar ta ce, kasashe mafiya hadari a farkon wannan shekara sun hada da Afghanistan, inda aka kashe 'yan jarida 11, sai Mexico 4, Syria 4, Ecuador 3, a Indiya da Yemen kuma an kashe 'yan jaridu uku-uku. Yayin da a kasashen Brazil da zirin Gaza da Guatemala da Pakistan kuma aka kashe 'yan jaridu bibbiyu. Sai kuma kasashen Colombia da Haiti, da Iraki da Liberiya da Nicaragua da Rasha da El-Salvador da Slovakia da aka kashe 'dan jarida daddaya kowanne. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China