in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya lashi takwabin samar da zaman lafiya a shiyyar
2018-05-03 09:55:32 cri

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya lashi takwabin ci gaba da jagorantar shirye-shiryen wanzar da zaman lafiyar shiyyar, domin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kasashen Sudan ta kudu da Somaliya.

Bugu da kari, Kenyatta ya kuduri aniyar karfafa dakarun tsaron kasar, ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu na samar da zaman lafiya. Yana mai cewa, idan har babu zaman lafiya, kasar Kenya ba za ta iya cimma manufofinta ba.

Ya ce, kasarsa na da burin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Sudan ta kudu ta Somliya, kasashe biyu makwabta da ke fama da matsalar tsaro.

Shugaban ya ce, Somliya na fama da tashin hankali sakamakon kutsen kasashen ketare, wadanda ke kokarin gurgunta gwamnatin kasar, da mayar da hannun agogo baya kan nasarorin da dakarun kungiyar AU dake aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya (AMISON) suka cimma, da ma raba kan al'ummun kasar. A don haka ya ce, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa Somaliyar, har sai an maido da kwanciyar hankali a kasar.

Shugaba Kenyatta ya ce, idan har 'yan uwanmu a Somaliya suka samu makoma da tsaro mai kyau, to mu ma mun tsira, manufarmu a nan ita ce, samar da tsaro da kwanciyar hankali, gami da makoma mai kyau a shiyyar baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China